<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>38</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Mun gode wa Allah da dukan zuciyarmu,
 Da waƙa mai daɗi domin duk ayyukansa.
 Tun muna jarirai, albarkarsa 'na nan.
 Da duk alheransa, yanzu ya dube mu.

[V2]
 2) Rayayyen Allahnmu tare da mu zai zauna.
 Muddar rayukanmu, shi zai albarkace mu.
 Kullum da alherai zai kiyaye mu duk.
 Zai tsare ƴaƴansa daga hatsari duk.

[V3]
 3) Yabo da hamdala ga Allahnmu na Sama,
 Da Ɗa Mai Cetonmu, Ruhunsa mai bishe mu. Duniya da Sama duk suna ta yabonsa
 A da, da yanzu kuwa, nan gaba abada.</lyrics>
<title>Mun Gode Wa Allah da Dukan Zuciyarmu LW38</title>
</song>